Job 37
1“Wannan ya sa gabana ya fāɗi,zuciyata ta yi tsalle.
2Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa,
tsawar da take fita daga bakinsa.
3Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai
ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya.
4Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo;
Ya tsawata da muryarsa mai girma.
Sa’ad da ya sāke yin tsawa
ba ya rage wani abu.
5Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi;
yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu.
6Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’
ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’
7Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa,
ya hana kowane mutum yin wahalar aiki.
8Dabbobi sun ɓoye;
sun zauna cikin kogunansu.
9Guguwa tana fitowa daga inda take,
sanyi kuma daga iska mai sanyi.
10Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara
sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara.
11Yana cika gizagizai da lema;
yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
12Bisa ga bishewarsa suke juyawa
a kan fuskar duniya,
suna yin dukan abin da ya
umarce su su yi.
13Yana aiko da ruwa domin horon mutane,
ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa.
14“Ka saurari wannan Ayuba;
ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
15Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai
ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka?
16Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama,
waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani.
17Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da
iska mai sanyi take hurawa,
18ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi
da ƙarfi kamar madubi?
19“Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa;
ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu.
20Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana?
Ko wani zai nemi a haɗiye shi?
21Yanzu ba wanda zai iya kallon rana,
yadda take da haske a sararin sama
bayan iska ta share ta.
22Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya,
Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi.
23Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu,
shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci,
ba ya cutar mutum.
24Saboda haka, mutane suke girmama shi,
ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?”
Copyright information for
HauSRK