Job 38
Ubangiji ya yi magana
1Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, 2“Wane ne wannan da yake ɓata mini shawaratada surutan wofi?
3Ka sha ɗamara kamar namiji;
zan yi maka tambaya,
za ka kuwa amsa mini.
4“Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?
Gaya mini, in ka sani.
5Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!
Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
6A kan me aka kafa tushenta,
ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
7yayinda taurarin safe suke waƙa tare
dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
8“Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi,
lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.
9Lokacin da na yi wa gizagizai riga
na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
10sa’ad da na yi masa iyaka na
sa masa ƙofofi da wurin kullewa.
11Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai,
ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?
12“Ko ka taɓa ba safiya umarni
ko kuma ka sa asuba ta fito,
13don ta kama gefen duniya
ta kakkaɓe mugaye daga cikinta?
14Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi;
ta fito a fili kamar riga.
15An hana mugaye haskensu,
hannun da suka ɗaga an karya shi.
16“Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku,
ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku?
17Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa?
Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa?
18Ko ka gane fāɗin duniya?
Gaya mini, in ka san wannan duka.
19“Ina ne hanyar zuwa gidan haske?
Kuma a ina duhu yake zama?
20Ko za ka iya kai su wurarensu?
Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama?
21Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin!
Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa.
22“Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara
ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara
23waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala,
domin kwanakin yaƙi da faɗa?
24Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya,
ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya?
25Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa,
da kuma hanyar walƙiyar tsawa
26don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin
jeji inda ba mai zama ciki
27don a ƙosar da wurin da ya bushe
a sa ciyawa ta tsiro a can?
28Ruwan sama yana da mahaifi?
Wa ya zama mahaifin raɓa?
29Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara?
Wane ne ya haifi jaura daga sammai
30lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse,
lokacin da saman ruwa ya daskare?
31“Za ka iya daure kyakkyawar kaza da’ya’yanta?
Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo?
32Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu
ko kuma ka bi da beyar da’ya’yanta zuwa waje?
33Ka san dokokin sammai?
Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya?
34“Za ka iya tsawata wa gizagizai
ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa?
35Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa?
Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’
36Wane ne yake cika zuciya da hikima
ko kuma yake ba zuciya ganewa?
37Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai?
Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai
38sa’ad da ƙura ta yi yawa
ta daskare a wuri ɗaya?
39“Za ka iya farauto wa zakanya nama,
ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu.
40Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu,
ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu?
41Wane ne yake ba hankaka abinci
lokacin da’ya’yansa suke kuka ga Allah,
kuma suna yawo don rashin abinci?
Copyright information for
HauSRK