Job 39
1“Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa?Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
2Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu?
Ka san lokacin da suke haihuwa?
3Suna kwanciya su haifi’ya’yansu;
naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
4’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji;
sukan tafi ba su dawowa.
5“Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi?
Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
6Na sa jeji yă zama gidansa
ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
7Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari;
ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
8Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa
yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
9“Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci?
Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
10Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya?
Zai yi maka buɗar gonarka?
11Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa?
Za ka bar masa nauyin aikinka?
12Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida
yă tattara shi a masussuka?
13“Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki
amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
14Tana sa ƙwai nata a ƙasa
kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
15ba tă damu ko za a taka su a fasa su,
ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
16Tana tsananta wa’ya’yanta kamar ba nata ba
ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
17Gama Allah bai ba ta hikima ba
ko kuma iya fahimta.
18Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu
tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
19“Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa
kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
20Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra,
ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
21Yana takawa da ƙarfi
yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
22Yana yi wa tsoro dariya
ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
23Kwari a baka yana lilo a gabansa
kibiya da māshi suna wuce kansa.
24Yana kartar ƙasa da ƙarfi;
ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
25Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’
Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa,
da ihun shugabannin yaƙi.
26“Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya
take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
27Ko da umarninka ne shaho yake firiya
ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
28Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare;
cikin duwatsu ne wurin zamansa.
29Daga can yake neman abincinsa;
idanunsa suna gani daga nesa.
30’Ya’yansa suna shan jini,
inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”
Copyright information for
HauSRK