‏ Job 41

1“Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi
ko kuma ka daure harshenta da igiya?
2Za ka iya sa igiya a cikin hancinta
ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya?
3Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai?
Ko za tă yi maka magana a hankali?
4Za tă yi yarjejjeniya da kai
don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta?
5Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu?
Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata?
6’Yan kasuwa za su saye ta
ko za su raba ta a tsakaninsu?
7Ko za ka iya huda fatarta da kibiya
ka kuma huda kansa da māsu?
8In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta
za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba!
9Duk ƙoƙarin kama ta banza ne;
ganin ta kawai abin tsoro ne.
10Ba wanda ya isa yă tsokane ta.
Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni?
11Wane ne yake bi na bashi da dole in biya?
Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne.

12“Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba
ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba.
13Wa zai iya tuɓe mata mayafinta?
Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta.
14Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta?
Haƙoranta ma abin tsoro ne?
15An rufe bayanta da jerin garkuwoyi
aka manne su sosai.
16Suna kurkusa da juna yadda
da ƙyar iska take iya wucewa tsakani.
17An haɗa su da juna
sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba.
18Numfashinta yana fitar da wuta;
idanunta kamar hasken zuwan safe.
19Wuta tana fitowa daga bakinta;
tartsatsin wuta suna fitowa,
20Hayaƙi yana fitowa daga hancinta
kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace.
21Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta,
harshen wuta yana fita daga bakinta.
22Akwai ƙarfi a cikin wuyanta;
razana tana wucewa a gabanta.
23Namanta yana da kauri a manne da juna;
naman yana da tauri ba ya matsawa.
24Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse,
da ƙarfi kamar dutsen niƙa.
25Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata;
suna ja da baya.
26Takobi ba ta iya yankanta,
kibiya ko māshi ba sa iya huda ta.
27Ƙarfe kamar kara ne a wurinta
tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta.
28Māsu ba su sa ta tă gudu;
jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta.
29Kulki a gare ta kamar ciyawa ne,
tana dariyar wucewar māshi.
30Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi,
tana kabtar ƙasa in tana tafiya.
31Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya,
ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa.
32A bayanta ya bar haske
kamar zurfin ruwan da yana kumfa.
33Ba wani abu kamar ta a duniya,
halitta marar tsoro.
34Tana rena duk masu girman kai.
Ita take mulki kan duk masu girman kai.”
Copyright information for HauSRK