Job 6
Ayuba
1Sa’an nan Ayuba ya amsa, 2“Da kawai za a iya auna wahalataa kuma sa ɓacin raina a ma’auni!
3Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi,
shi ya sa nake magana haka.
4Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina,
ruhuna yana shan dafinsa;
fushin Allah ya sauka a kaina.
5Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci,
ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta?
6Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba,
ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai?
7Na ƙi in taɓa shi;
irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya.
8“Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu,
da ma Allah zai biya mini bukatata,
9wato, Allah yă kashe ni,
yă miƙa hannunsa yă yanke raina!
10Da sai in ji daɗi
duk zafin da nake sha
ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba.
11“Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya?
Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
12Da ƙarfin dutse aka yi ni ne?
Ko jikina tagulla ne?
13Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne,
yanzu da aka kore nasara daga gare ni?
14“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki
ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
15Amma’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba,
kamar rafin da yakan bushe da rani,
16kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara,
yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke,
17amma da rani sai yă bushe,
lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin.
18Ayari sukan bar hanyarsu;
sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu.
19Ayarin Tema sun nemi ruwa,
matafiya’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu.
20Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai;
sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba.
21Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako;
kun ga abin bantsoro kuka tsorata.
22Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina,
ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku,
23ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina,
ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’?
24“Ku koya mini, zan yi shiru;
ku nuna mini inda ban yi daidai ba.
25Faɗar gaskiya tana da zafi!
Amma ina amfanin gardamar da kuke yi?
26Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne,
ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi?
27Kukan yi ƙuri’a a kan marayu
ku kuma sayar da abokinku.
28“Amma yanzu ku dube ni da kyau,
zan yi muku ƙarya ne?
29Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi;
ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi.
30Ko akwai wata mugunta a bakina?
Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba?
Copyright information for
HauSRK