‏ John 6:15-21

15Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

Yesu ya yi tafiya a kan ruwa

(Mattiyu 14.22-27; Markus 6.45-52)

16Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki, 17inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna. 18Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka. 19Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata. 20Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.” 21Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.
Copyright information for HauSRK