‏ Jonah 2

1Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa. 2Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji,
ya kuwa amsa mini.
Daga cikin zurfi kabari
Sheol na Ibraniyanci
na yi kiran neman taimako,
ka kuwa saurari kukata.
3Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku,
ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa;
dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka
sun bi ta kaina.
4Sai na ce, ‘An kore ni
daga fuskarka;
duk da haka zan sāke duba
wajen haikalinka mai tsarki.’
5Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana,
Ko kuwa ruwaye sun kai ga maƙoshina

zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni.
6Na nutsa har ƙarƙashin tuddai;
a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada.
Amma ka dawo da raina daga rami,
Ya Ubangiji Allahna.

7“Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni,
na tuna da kai ya Ubangiji,
addu’ata kuma ta kai gare ka,
a haikalinka mai tsarki.

8“Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani,
sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu.
9Amma ni, da waƙar godiya,
zan miƙa tawa hadaya gare ka.
Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi.
Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.”

10Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku.
Copyright information for HauSRK