‏ Judges 1:12-15

12Sai Kaleb ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat Sefer ya kuma ci ta da yaƙi, zan ba shi’yata Aksa yă aura.” 13Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kaleb ya ci birnin, saboda haka Kaleb ya ba shi’yarsa Aksa ya aura.

14Wata rana da ta zo wurin Otniyel, sai ta zuga shi
Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Bulget Otniyel, ya zuga ta
yă roƙi mahaifinta fili. Sa’ad da ta sauko daga jakinta, sai Kaleb ya ce mata, “Me zan yi miki?”

15Sai ta ce, “Ka yi mini alheri na musamman. Da yake ka ba ni ƙasa a Negeb, to, sai ka ba ni maɓulɓulan ruwa kuma.” Sai Kaleb ya ba ta maɓulɓulan bisa da kuma na ƙasa.
Copyright information for HauSRK