Lamentations 2
▼▼ Wannan surar waƙa ce mai bin harufa bi da bi, ayoyin da suka fara da harufan Ibraniyanci bi da bi.
1Yadda Ubangiji ya rufe Diyar Sihiyonada gizagizan fushi! ▼
▼Ko kuwa Yadda Ubangiji cikin fushinsa / ya yi da Diyar Sihiyona da wargi
Ya jefar da darajar Isra’ila
daga sama zuwa ƙasa;
bai tuna da wurin ɗora ƙafafunsa ba
a ranar fushinsa.
2Ubangiji ya hallakar
da wurin zaman Yaƙub ba tausayi;
A cikin fushinsa kuma zai rurrushe
kagaran Diyar Yahuda.
Ya ƙasƙantar da mulki
da masu mulki.
3A cikin zafin fushi ya fasa
kowane ƙaho na Isra’ila.
Ya janye hannun damansa
sa’ad da maƙiyi ya zo.
Ya yi ƙuna a cikin Yaƙub kamar wuta mai ƙone
duk abin da yake kusa da ita.
4Kamar abokin gāba, ya ɗana bakansa;
hannun damansa na shirye.
Kamar maƙiyi,
ya kashe duk wanda idonsa ya ji daɗin gani;
ya zuba fushinsa kamar wuta
a kan tenti na Diyar Sihiyona.
5Ubangiji kamar maƙiyi ne;
ya hallaka Isra’ila.
Ya hallaka wurarenta duka
ya kuma hallaka kagaranta.
Ya ƙara yawan makoki da baƙin ciki
wa Diyar Yahuda.
6Ya rushe haikalinsa kamar lambu;
ya hallaka wurin yi masa sujada.
Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta
da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci;
a cikin zafin fushinsa
ya watsar da sarki da firist.
7Ubangiji ya ƙi bagadensa
ya kuma yi wofi da haikalinsa.
Ya ba maƙiyinta fadodinta;
suka yi sowa a cikin gidan Ubangiji
kamar a ranar da ake yin biki.
8 Ubangiji ya ƙuduri niyya yă rushe bangon
da yake kewaye da Diyar Sihiyona.
Ya auna da igiyar awo
bai fasa hallaka ta ba.
Ya sa katanga da katanga
duk suka lalace.
9Ƙofofinta sun nutse a cikin ƙasa;
ya kakkarya ƙarafanta.
Sarakunanta da’ya’yan sarakunanta
duk an kai su bauta cikin waɗansu ƙasashe,
babu sauran doka,
annabawa kuma ba su samun
wahayi daga wurin Ubangiji.
10Dattawan Diyar Sihiyona
sun zauna shiru a ƙasa;
suka kuma sa rigar buhu.
’Yan matan Urushalima suka
sunkuyar da kawunansu ƙasa.
11Idanuna sun dushe don yawan kuka,
raina na cike da baƙin ciki;
zuciyata ta karaya
domin mutanena sun hallaka,
domin yara da jarirai suna suma
a kan hanyoyi a cikin birni.
12Suna ce wa uwayensu,
“Ina burodi da ruwan inabi?”
Yayinda suke suma kamar mutanen
da aka ji masu ciwo a cikin birni,
sa’ad da suke mutuwa
a hannuwan uwayensu.
13Me zan ce miki?
Da me zan kwatanta ki,
ke Diyar Urushalima?
Da me zan misalta ki,
yadda zan iya yi miki ta’aziyya,
Ke Budurwa Diyar Sihiyona?
Ciwonki yana da zurfi kamar teku.
Wane ne zai iya warkar da ke?
14Wahayin annabawanki
ƙarya ne kuma marasa amfani;
ba su tona zunubanki ba
yadda za su iya ceto ki daga bauta ba.
Sun yi miki annabcin ƙarya
marar amfani.
15Duk masu wucewa
suna yi miki tafi na reni;
suna yi wa Diyar Urushalima
tsaki suna kaɗa kai suna cewa,
“Wannan ne birnin da aka ce
kyakkyawa ne,
mai farantawa dukan duniya rai?”
16Maƙiyanki duka suna ta surutu
game da ke;
suna tsaki suna cizon haƙora
suna cewa, “Mun hallaka ta.
Wannan ce ranar da muke jira;
yau mun gan ta.”
17 Ubangiji ya yi abin da ya shirya;
ya cika maganarsa,
wadda ya umarta tun daɗewa.
Ya jefar da ke ba tausayi,
ya bari maƙiya sun yi nasara da ke,
ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.
18Zuciyar mutane
ta yi kuka ga Ubangiji.
Ya bangon Diyar Urushalima,
bar hawayenki su zuba kamar rafi
dare da rana;
kada ki huta,
kada idanunki su huta.
19Ki tashi, ki yi kuka cikin dare,
dare na yi sai ki fara kuka;
kina buɗewa Ubangiji zuciyarki.
Ki ɗaga hannuwanki gare shi
domin rayukan’ya’yanki,
waɗanda suka suma don yunwa
a kan kowane titi.
20“Ka duba, ka gani ya Ubangiji.
Wane ne ka taɓa yi wa haka?
Ko ya kamata uwaye su ci’ya’yansu,
’ya’yan da suka yi reno?
Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa
a cikin haikalin Ubangiji?
21“Matasa da tsofaffi duk
suna kwanciya a cikin ƙurar tituna;
an karkashe matasa
da’yan matana da takobi.
Ka kashe su a ranar fushinka;
ka kashe su ba tausayi.
22“Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki,
haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe.
A ranar fushin Ubangiji
ba mai tserewa ba wanda zai tsira;
maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu,
na kuma lura da su.”
Copyright information for
HauSRK