Lamentations 3
▼▼ Wannan surar waƙa ce; ayoyin kowane sakin layi sun fara da harufan Ibraniyanci bi da bi, kuma ayoyin cikin kowane sakin layi ya fara da harufa iri ɗaya.
1Ni ne mutumin da ya ga azabata wurin bulalar fushin Ubangiji.
2Ya kore ni, ya sa na yi tafiya
a cikin duhu maimakon a cikin haske;
3ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni
sau da sau, dukan yini.
4Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa
ya kuma karya ƙasusuwana.
5Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni
da baƙin ciki da kuma wahala.
6Ya sa na zauna a cikin duhu
kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
7Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba;
Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
8Ko lokacin da nake kira don neman taimako,
ba ya jin addu’ata.
9Ya tare hanyata da tubula na duwatsu;
ya sa hanyata ta karkace.
10Kamar beyar da take a laɓe tana jira,
kamar zaki a ɓoye,
11ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni
ya bar ni ba taimako.
12Ya ja kwarinsa
ya sa in zama abin baratarsa.
13Ya harbi zuciyata
da kibiyoyin kwarinsa.
14Na zama abin dariya ga mutanena duka;
suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
15Ya cika ni da kayan ɗaci
ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
16Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa;
ya tattake ni cikin ƙura.
17An hana ni salama;
na manta da ko mene ne ake kira wadata.
18Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare
da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
19Na tuna da azabata da kuma sintiri,
da na yi ta yi da ɗacin rai.
20Na tuna su sosai,
sai kuma na ji ba daɗi a raina.
21Duk da haka na tuna da wannan
na kuma sa bege ga nan gaba.
22Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba;
gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
23Sababbi ne kowace safiya;
amincinka kuwa mai girma ne.
24Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa;
saboda haka zan jira shi.”
25 Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa,
ga kuma wanda yake neman shi;
26yana da kyau ka jira shiru
domin samun ceton Ubangiji.
27Yana da kyau mutum yă sha wuya
tun yana yaro.
28Bari yă zauna shiru shi kaɗai,
gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
29Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura
kila akwai bege.
30Bari yă ba da kumatunsa a mare shi,
yă kuma bari a ci masa mutunci.
31Gama Ubangiji ba ya
yashe mutane har abada.
32Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai,
ƙaunarsa tana da yawa.
33Gama ba haka kawai yake kawo wahala
ko ɓacin rai ga’yan adam ba.
34Bai yarda a tattake
’yan kurkuku a ƙasa ba,
35ko kuma a danne wa mutum hakkinsa
a gaban Maɗaukaki,
36ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya
ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
37Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika
in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38Ba daga bakin Maɗaukaki ne
bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
39Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni
sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
40Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta,
sai mu kuma koma ga Ubangiji.
41Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu
ga Allah na cikin sama, mu ce,
42“Mun yi zunubi mun yi tawaye
ba ka kuwa gafarta ba.
43“Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu;
ka karkashe mu ba tausayi.
44Ka rufe kanka da gajimare
don kada addu’armu ta kai wurinka.
45Ka mai da mu tarkace da juji
a cikin mutane.
46“Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana
marar daɗi.
47Muna cika da tsoro,
da lalatarwa da hallakarwa.”
48Hawaye na kwararowa daga idanuna
domin an hallaka mutanena.
49Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye,
ba hutawa.
50Har sai in Ubangiji ya duba
daga sama ya gani.
51Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki
domin dukan matan birnina.
52Maƙiyana suna farauta ta
ba dalili kamar tsuntsu.
53Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami
suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
54ruwaye suka rufe kaina,
sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
55Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji,
daga rami mai zurfi.
56Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka
ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
57Ka zo kusa lokacin da na kira ka,
kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
58Ya Ubangiji, ka goyi bayana;
ka fanshi raina.
59Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba.
Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
60Ka ga zurfin ramakonsu,
da duk mugun shirin da suke yi mini.
61Ya Ubangiji, ka ji zaginsu,
da duka mugun shirin da suke yi mini
62Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai
game da ni duk yini.
63Dube su! A zaune ko a tsaye,
suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
64Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji,
domin abin da hannuwansu suka yi.
65Ka sa yana ta rufe zuciyarsu,
kuma bari la’anarka ta bi su.
66Ka fafare su cikin fushi
ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK