Lamentations 5
1Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu;duba, ka ga kunyar da muka sha.
2An ba wa baƙi gādonmu,
gidajenmu kuma aka ba bare.
3Mun zama marayu marasa ubanni,
uwayenmu kamar gwauraye.
4Dole mu sayi ruwan da muke sha;
sai mun biya mu sami itace.
5Masu fafararmu sun kusa kama mu;
mun gaji kuma ba dama mu huta.
6Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya
don mu sami isashen abinci.
7Kakanninmu sun yi zunubi
kuma ba sa nan yanzu,
mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.
8Bayi suna mulki a kanmu,
kuma ba wanda zai’yantar da mu daga hannuwansu.
9Muna samun burodi a bakin rayukanmu
domin takobin da yake a jeji.
10Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,
muna jin zazzaɓi domin yunwa.
11An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona,
da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.
12An rataye’ya’yan sarakuna da hannuwansu;
ba a ba wa dattawa girma.
13Samari suna faman yin niƙa;
yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.
14Dattawan sun bar ƙofar birnin,
samari sun daina rera waƙa.
15Farin ciki ya rabu da zuciyarmu;
rayuwarmu ta zama makoki.
16Rawani ya fāɗi daga kanmu.
Kaiton mu gama mun yi zunubi!
17Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi;
domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe
18gama Tudun Sihiyona ya zama kufai,
sai diloli ke yawo a wurin.
19Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada;
kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.
20Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe?
Me ya sa ka yashe mu da jimawa?
21Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo;
ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā
22sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya
kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.
Copyright information for
HauSRK