‏ Leviticus 23:26-32

Ranar kafara

(Ƙidaya 29.7-11)

26 Ubangiji ya ce wa Musa, 27“Rana ta goma ta wata bakwai, za tă zama Ranar Kafara. Sai ku yi taro mai tsarki don ku yi mūsun kanku ku kuma miƙa hadayar da aka yi da wuta ga Ubangiji. 28Kada ku yi aiki a ranar, gama Ranar Kafara ce, sa’ad da za a yi kafara saboda ku a gaban Ubangiji Allahnku. 29Duk wanda bai yi mūsun kansa a wannan rana ba, dole a raba shi daga mutanensa. 30Zan hallaka duk wani da ya yi aiki a wannan rana daga mutanensa. 31Sam ba za ku yi wani aiki ba. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce, wa tsararraki masu zuwa, a ko’ina kuke da zama. 32Asabbaci ne na hutu dominku, kuma dole ku yi mūsun kanku. Daga yamman rana ta tara ga wata, har zuwa yamma na biye, za ku kiyaye Asabbacinku.”
Copyright information for HauSRK