Leviticus 24:1-4
Mai da burodi, shiryayye a gaban Ubangiji
(Fitowa 27.20,21)
1 Ubangiji ya ce wa Musa, 2“Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba. 3Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa. 4Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.
Copyright information for
HauSRK