‏ Luke 10:13-15

(Mattiyu 11.20-24)

13 “ ‘Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin rigar makoki da toka. 14A ranar shari’a, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku. 15Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki.
Copyright information for HauSRK