Luke 10:25-28
Misalin mutumin Samariya nagari
25Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” 26Yesu ya amsa ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?” 27Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” 28Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”
Copyright information for
HauSRK