Luke 11:24-26
(Mattiyu 12.43-45)
24 “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ 25Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye. 26Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”
Copyright information for
HauSRK