Luke 19:45-48
Yesu a haikali
(Mattiyu 21.12-17; Markus 11.15-19; Yohanna 2.13-22)
45Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. 46Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’ ▼▼Ish 56.7
amma ga shi kun mai da shi ‘kogon’yan fashi.’ ” ▼▼Irm 7.11
47Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. 48Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.
Copyright information for
HauSRK