‏ Luke 21:29-33

(Mattiyu 24.32-35; Markus 13.28-31)

29Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa. 30A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa. 31Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.

32 “Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika. 33Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
Copyright information for HauSRK