Luke 22:3-6
3Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. 4Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su. 5Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi. 6Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.
Copyright information for
HauSRK