Luke 22:31-34
(Mattiyu 26.31-35; Markus 14.27-31; Yohanna 13.36-38)
31 “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka ▼▼ Girik yana da ku ne a nan
kamar alkama. 32Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa’yan’uwanka.” 33Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.” 34Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”
Copyright information for
HauSRK