Luke 23:3-5
3Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.” 4Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.” 5Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.”
Copyright information for
HauSRK