‏ Luke 5:27-32

Kiran Lawi

(Mattiyu 9.9-13; Markus 2.13-17)

27Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” 28Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.

29Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su. 30Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

31Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 32Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
Copyright information for HauSRK