‏ Luke 6:20-23

(Mattiyu 5.1-12)

20Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta,
gama mulkin Allah naku ne.
21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,
gama za ku ƙoshi.
Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,
gama za ku yi dariya.
22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,
suka ware ku, suka zage ku,
suna ce da ku mugaye,
saboda Ɗan Mutum.

23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.
Copyright information for HauSRK