Luke 6:43-45
Itace da’ya’yansa
(Mattiyu 7.17-20; 12.34,35)
43 “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da’ya’ya masu kyau. 44Kowane itace da irin’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. 45Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
Copyright information for
HauSRK