Luke 6:6-11
(Mattiyu 12.9-14; Markus 3.1-6)
6A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. 7Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. 8Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya. 9Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?” 10Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. 11Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu.
Copyright information for
HauSRK