‏ Luke 8:19-21

Mahaifiyar Yesu da’yan’uwansa

(Mattiyu 12.46-50; Markus 3.31-35)

19Sai uwar Yesu da’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron. 20Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”

21Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
Copyright information for HauSRK