Luke 9:22-27
22Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.” 23Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni. 24Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi. 25Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa. 26Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun. 27 “Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”
Copyright information for
HauSRK