Mark 11:12-14
Yesu ya tsabtacce haikali
(Mattiyu 21.18,19)
12Kashegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa. 13Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yă ga ko yana da’ya’ya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin’ya’yan ɓaure ba ne. 14Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yă ƙara cin’ya’yanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
Copyright information for
HauSRK