‏ Mark 13:14-19

(Mattiyu 24.15-21; Luka 21.20-24)

14 “Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’
Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11
tsaye inda
Ko kuwa shi; haka ma a aya 29
bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.
15Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. 16Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. 17Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon’ya’ya a waɗancan kwanakin! 18Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. 19Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.
Copyright information for HauSRK