‏ Mark 13:24-27

(Mattiyu 24.29-31; Luka 21.25-28)

24 “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za tă yi duhu,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25 taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.
Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
Ish 13.10; Ish 34.4

26 “Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. 27Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.
Copyright information for HauSRK