‏ Mark 13:28-31

(Mattiyu 24.32-35; Luka 21.29-33)

28 “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 30Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. 31Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
Copyright information for HauSRK