‏ Mark 14:3-9

(Mattiyu 26.6-13; Yohanna 12.1-8)

3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.

4Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? 5Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi
Girik fiye da dinari ɗari uku
ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”

6Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. 7Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. 8Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata. 9Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
Copyright information for HauSRK