‏ Mark 14:66-68

Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu

(Mattiyu 26.69-75; Luka 22.56-62; Yohanna 18.15-18,25-27)

66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. 67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau.

Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”

68Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ƙofar shiga zakara kuwa ya yi cara
Copyright information for HauSRK