‏ Mark 14:69-72

69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70Sai ya sāke yin musu.

Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”

71Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”

72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu.
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau na biyu.
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu,
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu.
za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.
Copyright information for HauSRK