‏ Mark 15:16-21

Sojoji sun yi wa Yesu ba’a

(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)

16Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. 17Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. 18Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 19Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. 20Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.

Gicciyewa

(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)

21Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.
Copyright information for HauSRK