Mark 3:13-19
Naɗin manzanni sha biyu
(Mattiyu 10.1-4; Luka 6.12-16)
13Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa. 14Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni ▼▼Waɗansu rubuce-rubucen hannu ba su da kira su manzanni.
don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, 15don kuma su sami ikon fitar da aljanu. 16Ga sha biyun da ya naɗa.Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);
18Andarawus,
Filibus,
Bartolomeyu,
Mattiyu,
Toma,
Yaƙub ɗan Alfayus,
Taddayus,
Siman wanda ake kira Zilot,
19da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
Copyright information for
HauSRK