Mark 3:31-35
Mahaifiyar Yesu da’yan’uwansa
(Mattiyu 12.46-50; Luka 8.19-21)
31Sai mahaifiyar Yesu tare da’yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki yă kira shi. 32Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Mahaifiyarka da’yan’uwanka suna waje, suna nemanka.” 33Ya yi tambaya ya ce, “Su wane ne mahaifiyata, da’yan’uwana?” 34Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, “Ga mahaifiyata da’yan’uwana! 35Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da’yar’uwata, da kuma mahaifiyata.”
Copyright information for
HauSRK