‏ Mark 4:10-12

(Mattiyu 13.10-17; Luka 8.9,10)

10Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. 11Sai ya ce musu, “An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai. 12Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba,
kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba,
in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”
Ish 6.9,10

Copyright information for HauSRK