Mark 4:21-25
Fitila a kan wurin ajiye fitila
(Luka 8.16-18)
21Sai ya ce musu, “Ko kukan kawo fitila ku rufe ta da murfi ko kuma ku sa ta a ƙarƙashin gado ne? Ba kukan sa ta a kan wurin ajiye fitila ba? 22Duk abin da yake a ɓoye, dole za a fallasa shi. Duk abin da kuma yake a rufe, dole za a fitar da shi a fili. 23Duk mai kunnen ji, bari yă ji.” 24Ya ci gaba da cewa, “Ku lura da abin da kuke ji da kyau. Mudun da ka auna da shi, da shi za a auna maka, har ma a ƙara. 25Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda kuma ba shi da shi, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
Copyright information for
HauSRK