‏ Mark 6:1-6

Annabi marar daraja

(Mattiyu 13.53-58; Luka 4.16-30)

1Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. 2Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki.

Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!
3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe,’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

4Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” 5Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su. 6Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu.

Yesu ya aiki sha biyun

(Mattiyu 10.5-15; Luka 9.1-6)

Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
Copyright information for HauSRK