Mark 6:7-13
7Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi. 8Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.” 12Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. 13Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
Copyright information for
HauSRK