‏ Mark 8:27-29

Shaidar Bitrus a kan Kiristi

(Mattiyu 16.13-20; Luka 9.18-21)

27Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”

28Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Iliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.”

29Sai ya yi tambaya ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?”

Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.
Ko kuwa Almasihu “Kiristi” (da Girik) “Almasihu” kuma (da Ibraniyanci) duk suna nufin “Shafaffen nan.”
Copyright information for HauSRK