‏ Mark 9:2-8

Sāke kamannin Yesu

(Mattiyu 17.1-13; Luka 9.28-36)

2Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna tare da shi, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, suka kasance su kaɗai a wurin. A can aka sāke kamanninsa a gabansu. 3Tufafinsa suka zama fari suna ƙyalli, fiye da yadda wani a duniya zai iya yi su. 4Iliya da Musa suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

5Bitrus ya ce wa Yesu, “Rabbi, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” 6(Bai san abin da zai faɗa ba ne, gama sun tsorata ƙwarai.)

7Sai wani girgije ya bayyana, ya rufe su, wata murya kuma ta fito daga girgijen, ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna, ku saurare shi!”

8Farat ɗaya, da suka waiwaya, ba su ƙara ganin kowa tare da su ba, sai dai Yesu.
Copyright information for HauSRK