Matthew 10:28-31
28Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta. 29Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku. 30Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su. 31Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
Copyright information for
HauSRK