‏ Matthew 12:46-50

Mahaifiyar Yesu da’yan’uwansa

(Markus 3.31-35; Luka 8.19-21)

46Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”
Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da aya 47.

48Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma’yan’uwana?” 49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma’yan’uwana. 50Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”
Copyright information for HauSRK