Matthew 14:22-27
Yesu ya yi tafiya a kan ruwa
(Markus 6.45-52; Yohanna 6.15-21)
22Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron. 23Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai, 24jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi. 25Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin. 26Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.” 27Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
Copyright information for
HauSRK