Matthew 18:6-9
(Markus 9.42-48; Luka 17.1,2)
6 “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku. 7Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su! 8In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu. 9In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.
Copyright information for
HauSRK