‏ Matthew 20:29-34

Makafi biyu sun sami ganin gari

(Markus 10.46-52; Luka 18.35-43)

29Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

31Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

32Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

33Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

34Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
Copyright information for HauSRK