‏ Matthew 21:12-17

Yesu a haikali

(Markus 11.15-19; Luka 19.45-48; Yohanna 2.13-22)

12Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’
Ish 56.7
amma kuna mai da shi ‘kogon’yan fashi.’ ”
Irm 7.11

14Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

16Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai
kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”
Zab 8.2

17Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.
Copyright information for HauSRK