‏ Matthew 23:37-39

(Luka 13.34,35)

37 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi. 38Ga shi, an bar muku gidanku a yashe. 39Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”
Zab 118.26
Copyright information for HauSRK